Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya? 1
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga […]
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Kafa hukumar ya dace – Muhammad Kabir
Muhammad Kabir Suleja: “Kafa hukumar ya dace ko don magance wulakancin da wasu mazaje ke yi wa mata a lokacin da suka sake su, ta hanyan tilasta masu barin gidajensu a gaggauce, alhali shari’a ta nuna cewa su zauna su yi zaman iddarsu a gidan mazajen da suka rabu da su tukuna. A wannan dan tsakani, idan an dace sai a samu sauyin ra’ayi su sabunta aurensu. Hukuma ce kadai za ta iya tilasta wa kowa bin ka’ida, sabanin abin da ke faruwa a mafi yawan lokuta a yanzu.”