Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya? 2
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga […]
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Ina goyon bayan kafa su – Idris Waziri
Malam Idris Waziri: “Ya dace a kafa su saboda yadda sakin aure ya yi yawa. Kuma idan aka kafa su babu shakka za a rage sake-saken aure a Arewa da kasa baki daya. Gaskiya ina goyon bayan kafa su dari-bisa-dari kuma ba na shakkun cewa za su yi maganin matsalar sakin aure.”