Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya? 3

A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga […]

Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya? 3
Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya? 3

A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Kafa hukumar zai magance matsalar sakin aure – Auwalu Azare

Auwalu Azare: “Ya kamata a kafa su saboda wasu mazan suna yin sakin auren ne bisa jahilci ko rashin fahimta. Idan ka duba za ka ga cewa wasu mazan suna yin auren ne saboda wata manufa, idan ba su sami biyan bukata ba sai su saki matan. Ka ga idan aka kafa irin wadannan hukumomi da kotuna za a yi maganin matsalar sakin aure.”