Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya? 4
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga […]
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Kafa hukumar zai taimaki al’umma – Imamu Suleiman
Imamu Suleiman Aliyu: “Ya dace a kafa hukumar sa ido a kan yawaitar mutuwar aure. Hukumar za ta sa ido a kan yawan mutuwar aure. Za ta iya jawo hankalin ma’aurata da kuma yi masu nasiha ba tare da sai an je kotu ba, domin wasu daga mazaje suna ganin gurfana a gaban kotu tonon asiri ne; don haka komai gaskiyar mace idan ta kai namiji kotu, wannan yakan tunzura shi ya sake ta. Amma idan akwai hukuma da ake tunani za ta iya, to ya dace a kafa domin ta rage mutuwar aure da ya yawaita a yanzu.”