Ko ya dace a kafa hukuma da kotunan kula da sakin aure a Najeriya? 5
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga […]
A yayin gudanar taron tattauna al’amuran kasa, Sanata dansadau ya bayar da shawarar cewa ya dace a kafa hukuma da kotuna masu zaman kansu, wadanda za su kula da al’amuran sakin aure a kasar nan. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a yi haka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Kafa hukumar ba zai yi tasiri ba – Alhaji Saleh
Alhaji Saleh Mawarki Pz: “Jin tsoron Allah shi zai hana mutuwar aure ba kafa hukuma ba. Mu ji tsoron Allah gaba dayanmu. Gudanar da binciken ma’aurata kafin kulla aure, kulla gaskiya, yarda tsakanin ma’aurata, sanin asali, guje wa duk abin da bai dace da shari’a ba kafin kulla aure kuma saboda zamani a gabatar da binciken duk wata cuta da ake gudun faruwarta kafin kulla auren, hakuri da samu ko rashin sa, tsare gaskiya ga ma’aurata tare da jin tsoron Allah; ya fi duk wani kafa hukumar sa ido da za a yi a kan mutuwar aure. Domin yanzu mafiya yawan zaurawan da ake da su, wasu mazajensu kashe su aka yi, wasu ko bacewa suka yi, ba wai mutuwar aure ba ne.”