Ko ya dace a kafa hukumar kayyade farashin muhimman kayan masarufi?
Ganin irin yadda ’yan kasuwa ke saka farashin da suka ga dama a kowane irin kayan masarufi, wannan ta sanya wasu suna kiran da a kafa hukumar kayyade farashi a kasar nan. Wasu kuma suna ganin a bar kasuwar bude, kowane kaya ya sama wa kansa darajar farashi. Abin tambaya a nan shi ne, ko […]
Ganin irin yadda ’yan kasuwa ke saka farashin da suka ga dama a kowane irin kayan masarufi, wannan ta sanya wasu suna kiran da a kafa hukumar kayyade farashi a kasar nan. Wasu kuma suna ganin a bar kasuwar bude, kowane kaya ya sama wa kansa darajar farashi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a kafa irin wannan hukuma ko kuwa? Ga abin da mabambantan mutane suke cewa:
Ina goyon bayan a kafa hukumar -Ali Maigoro
Adam Umar, a Abuja
Alhaji Ali Maigoro: “Ina goyon bayan kafa hukumar, domin na yi kasuwanci a lokacin da hukumar ke aiki a baya kuma na ga alfanunta; dan kasuwa ya samu mai saya ya samu. Ba za a sayar da kaya a farashi kaza ba a nan sannan a can a sayar da shi a wani farashin. Wannan zai shafi har da farashin mai, yadda aka saye shi a gidan mai haka za a saye shi a kasuwar bayan fage.”
Bai kamata a kafa hukumar ba- Halliru Jibrin
Adam Umar, a Abuja
Alhaji Halliru Jibrin: “Ba na goyon bayan kafa hukumar, a bar kasuwa ta sayar da kanta. Ai wanda ya sayo kaya shi ya san farashinsa. A duk wani abu da ka sani da ake sayarwa, akwai giredi, akwai kwashe, akwai kuma na tsaka-tsakiya kuma kowane dan kasuwa da irin wanda yake sayowa a cikin ukun, gwargwadon nau’i na jama’a da yake hulda da su. To, yaya za a ce za a kayyade masu farashi?”
kayyade farashi ya dace -Mansur Makama
Nasiru Bello, a Sakkwato
Mansur Makama: “Maganar gaskiya, hakan ya dace in za a mayar da matakin albashi iri daya, wanda ke aiki a Gwamnatin Tarayya da mai yi a jiha da kananan hukomomi; kada a bambanta albashinsu matukar matakin aikinsu daya. Domin duk kasuwa daya suke shiga, kaya daya suke amfani da su. Matukar gwamnati ta gaza yin haka, to bai kamata a kayyade kudin kayan masarufi ba. Misali, kai kana karbar dubu takwas, wannan yana karbar 18, ku je sayen shinkafa da aka kayyade wa kudi dubu shida, to ka ga wani zai samu sauki wani ko zai sha wuya ke nan.”
Kafa hukumar bai dace ba – Nasiru Musa
Nasiru Bello, a Sakkwato
Nasiru Musa: “A gaskiya wannan matakin da ake nufi a dauka bai dace ba, idan aka yi la’akari da wannan lokacin da kasa take yunkurin farfadowa. Ni a ganina, wannan dokar idan an kafa ta, akasarin wadanda za su koka kuwa talakawa ne. Da wannan nake ganin cewa in har da talakawa ya zama abin tausayi gare su don a yanzu buhun dawa ana sayensa kan kudi N8,500 zuwa gaba sai dai ka ga ana rububin sayen garin kwaki. Allah ya kawo muna sauki, amin.”
Lokacin kafa hukumar ya yi – Musa Usman
A.A. Masagala, a Benin
Malam Musa Usman: “A gaskiya a yanayin yadda aka tsinci kai a ciki, ina ganin ya kamata gwamnati ta shigo ta dauki matakin kafa hukumar da za ta kayyade farashin duk kaya mai muhimmanci ga rayuwar al’ummar kasa, domin kada a sake komawa gidan jiya. Saboda haka, kayyade farashin zai kawo karshen wahalar da ake fama a ciki kuma zai samar wa talaka sauki a cikin harkar rayuwarsa. Bayan zaman lafiyar da aka fara samu, idan gwamnatin ta yi wannan to ta yi wa talaka komai. Dalilina shi ne, ganin yadda ’yan kasuwa marasa imani suka kaifafa wukakensu, suna ci gaba da cin karensu babu babbaka da tsawwala farashin kaya ba tare da tunanin abin da hakan zai biyo daga baya ba. Don haka, ni ina goyon bayan gwamnati dari-bisa-dari, idan ta bullo da wannan tsarin na kayyade farashi a kasar nan.”
Kafa hukumar ya dace – Musa Abubakar
A.A. Masagala, a Benin
Musa Abubakar Gangwaso: “Ni ina ganin kafa hukumar kayyada farashin kayan masarufi a kasar nan ya dace kuma zai kara wa gwamnati farin jini tare da kawo karshen irin halin da talakawa suka tsinci kansu a ciki na tsawwalar farashin kaya mara kan gado da wasu miyagun ’yan kasuwa suka bullo da shi, da nufin shafa wa gwamnati mai ci bakin fenti. Saboda haka ya kamata kafin gwamnatin ta kirkiro hukumar kayyade farashin kaya, to ta fara da yin odar kayan masarufin kuma ta farfado da darajar Naira da bai wa masu karfin aljihu damar su shigo da muhimman kaya. Muddin gwamnati ta yi hakan kuma sai ta kayyade farashin kayan, domin muddin aka ce babu ka’ida ta gwamnati a kan farashi; abin da ake sayarwa na amfanin jama’a na yau da kullum, to al’umma na iya shiga wani yanayi. Don haka kayyade farashin kayan yana da muhimmanci ga al’ummar kasa.