Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka?
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka: Bai dace a kara wa jihohi karfi ba – Rasheed Shobowale Alhaji Rasheed Shobowale: “Ni a ganina wannan ba dace ba saboda ba mu da bin doka da oda kamar […]
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka:
Bai dace a kara wa jihohi karfi ba – Rasheed Shobowale
Alhaji Rasheed Shobowale: “Ni a ganina wannan ba dace ba saboda ba mu da bin doka da oda kamar kasashen da suka ci gaba, kuma kar ka manta cewa abu ne da muka saba da shi; sabanin sauran kasashen da suka ci gaba da suka saba bin doka sau da kafa fiye da mu ’yan Najeriya. Kar ka manta, idan an ce a yi wannan sabon tsarin, wannan yana nufin cewa hatta jihohi za su mallaki ’yan sandansu ne kuma me kake gani cewa idan yau a ce jihohi sun mallaki ’yan sanda, da za a bi dokar da oda ne, wannan tsari ne mai kyau amma ba mu faro da shi ba, a ce a yi yanzu, za a sha wuya domin mun saba da son banza.”