Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 02

Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka: Rage wa tarayya karfi bai dace ba – Ibrahim Waziri Ibrahim Waziri: “A fahimtata, ban goyi bayan rage wa Gwamnatin Tarayya karfi ba domin kara wa jihohi kuma in muka […]

Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 02
Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 02

Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka:

Rage wa tarayya karfi bai dace ba – Ibrahim Waziri

Ibrahim Waziri: “A fahimtata, ban goyi bayan rage wa Gwamnatin Tarayya karfi ba domin kara wa jihohi kuma in muka ajiye hankalinmu da kyau, za mu ga Gwamnatin Tarayyako a tsarin kundin kasar nan ta wuce wasa fa da har wani zai yi tunanin rage mata karfi. Kai ba ma shi ba, wakilan Gwamnatin Tarayya fa ba wani wuri ne za a je a samo su ba fa, ’yan jihohi ne za a je a zabo. To ka ga da wakilan jihohi kusan abu guda ne, sunan ne da wakilcin dai ke da bambanci amma tushen guda ne.”