Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 1
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka: kara wa jihohi karfi ya dace – Gafar Jimoh Gafar Jimoh: “Wannan ita ce dimokaradiyya da kasashen Turai suke amfani da ita. Ka ga kasashe irin su Amurka da ita […]
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka:
kara wa jihohi karfi ya dace – Gafar Jimoh
Gafar Jimoh: “Wannan ita ce dimokaradiyya da kasashen Turai suke amfani da ita. Ka ga kasashe irin su Amurka da ita ce suke amfani, inda Gwamnatin Tarayya ba ta da karfi kamar jihohi ko kuma kananan hukumomi. Wannan tsarin yana nufin kowace jiha za ta dogara ga abin da ta mallaka, sai dai ta bai wa Gwamnatin Tarayya gudunmowarta. Gaskiya da wannan tsarin ake bi kila da tuni mun yi nisa domin idan Gwamnatin Tarayya ba ta da karfi, kananan hukumomi su ne suka fi kusa da jama’a kuma su ne suka san matsalar mutane. Haka ma jihohi, kudin da ake kashewa wajen tafiyar da Gwamnatin Tarayya zai ragu ainun, don haka wannan tsari ne mai kyau.”