Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 3

Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka: Rage wa tarayya karfi ya dace – Aminu Ibrahim Alhaji Aminu Ibrahim “Bai kamata Gwamnatin Tarayya ta fi jihohi karfi ba, don haka abu ne mafi dacewa a rage mata […]

Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 3
Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 3

Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka:

Rage wa tarayya karfi ya dace – Aminu Ibrahim

Alhaji Aminu Ibrahim “Bai kamata Gwamnatin Tarayya ta fi jihohi karfi ba, don haka abu ne mafi dacewa a rage mata karfi. Domin ko ba komai dai jihohi su samu karfi zai sa kowa ya gamsu. Don haka a taron sanin makomar kasa, ind ai har ba wai taron siyasa ba ne, to a rage wa tarayya karfi a kara wa jihohi. Ni ba na tare da wannan kashin dankali, in har aka bari Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da rinjayar jihohi; ba za a samu cin nasara ba kuma duk wani talakka mai kishin kasar nan ba zai gamsu da yadda hakan za ta kasance ba.”