Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 4
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka: Ya kamata a rage wa tarayya karfi – Isa Sulaiman Isa Sulaiman dan Agaji: “A ganina, ya kamata a gyara tsarin dokokin; inda ya kamata a rage wa Gwamnatin Tarayya […]
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka:
Ya kamata a rage wa tarayya karfi – Isa Sulaiman
Isa Sulaiman dan Agaji: “A ganina, ya kamata a gyara tsarin dokokin; inda ya kamata a rage wa Gwamnatin Tarayya karfi, a kara wa gwamnatocin jihohi amma batun tsaro, ya kamata a samar wa jami’an tsaro ikon gudanar da ayyukansu da kuma kudinsu kai tsaye ba tare da katsalandan na Gwamnatin Tarayya ba. Kuma a bar kowa ya yi aikinsa ba tare da katsalandan ba, saboda yanzu zargin juna tsakanin gwamnatocin ya yi yawa don haka fadanci ya yi yawa, ba ci gaba kowa na shiga aikin kowa. Kuma duk gyaran da za a yi an san abin da ya dace da hanyoyin da aka bi a baya ake zaune lafiya. Don haka a bi gaskiya, a nisanci son zuciya sai a samu mafita daga kowane bala’i.”