Ko ya dace a kara wa jihohi karfi a rage wa Gwamnatin Tarayya ko a bar tsarin haka? 5
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka: Rage wa tarayya karfi ne alheri – Mukhtar Sarkin Fada Alhaji Mukhtar Sarkin Fada: “Ina goyon bayan a gyara tsarin dokokin tarayya da jihohi a taron kasa amma a yi […]
Wannan shi ne da muka tattauna a Muhawararmu ta wannan makon. Ga yadda muhawarar ta kasance daga wasu daga cikin Jihohin kasar nan kamar haka:
Rage wa tarayya karfi ne alheri – Mukhtar Sarkin Fada
Alhaji Mukhtar Sarkin Fada: “Ina goyon bayan a gyara tsarin dokokin tarayya da jihohi a taron kasa amma a yi a hankali wajen ganin an cire son zuciya tare da yin abin da ya dace. Amma yanzu akwai gyara sosai da ya kamata a yi. Musamman ya kamata a duba yadda gwamnoni ke wahala da talakawa wajen ciyar da su gaba, a inganta musu yadda za su taimaki mutanensu tare kuma da samar da gyara kan yadda ake kasafta kudin kasa. A bar ikon gudanar da dokoki a hannun majalisu da kuma sakar wa kowace hukuma mara ta yi aikin da ya dace domin jama’ar kasa ba tare da katsalandan na Gwamnatin Tarayya ba.