Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Bai dace a kara jami’o’i […]
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Bai dace a kara jami’o’i ba -Nasiru Babi Sakkwato
Nasiru Babi Sakkwato: “Muna da jami’o’i da yawa wadanda rashin kulawa ce babbar matsalarsu. Idan za a kula da su da malamansu, to da sai a gano cewa shin karancin makarantu ne ko kuma rashin kulawa? Mu dubi yadda filayen jami’o’i, musammam a Arewa suke da fadi, ba tare da wani gini a cikinsu ba. A gine filayen ta yadda za a kara filin daukar dalibai ya fi tulin tsintsiyar da ba za ta yi shara ba.”