Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?1

A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: A inganta tsofaffin maimakon kara […]

Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?1
Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?1

A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

A inganta tsofaffin maimakon kara wasu – Mustapha Sa’idu
Mustapha Sa’idu Muhammad: “A inganta tsofaffin jami’oin da muke da su a kasar nan a yanzu, a maimakon kafa wasu sabbi. Ni dai ba na goyan bayan kafa wasu jami’oi domin ba shi da wani amfani. Kamata ya yi gwamnati ta samar da hanyoyin da ya dace domin inganta ilimi a kasar nan, in yaso daga baya sai a san abin da za a yi. Amma ni dai gaskiya ba na goyan bayan wannan kiraye-kiraye da wasu ke yi na kafa jami’oi.”

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50