Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?2
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Bai kamata a kara yawan […]
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Bai kamata a kara yawan jami’o’i a Najeriya ba – Bashir Abu Sabe
Malam Bashir Abu Sabe: “Ni a ra’ayina, bai kamata a kara yawan jami’o’i a Najeriya ba saboda wadannan dalilai: Na daya, babu yawan malaman da za su kula da kowane sashe. Na biyu, babu isassun kayan aiki da za a sanya a dakunan gwaje-gwaje. Na uku, kasafin kudin da gwamnati ke ware wa sashen ilimi ya yi kadan, wanda wannan ke haifar da rashin isassun kudin tafiyar da jami’o’in da ke akwai yanzu haka. Don haka gara a inganta wadanda ake da su yanzu, maimakon kara gina wasu.”