Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?3
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Ya dace a kara yawansu […]
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Ya dace a kara yawansu
– Ibrahim Yeldu
Alhaji Ibrahim Yeldu: “An samu gagarumin ci gaba, wanda ma ba zai kirgu kai tsaye bad a yawan jami’o’i. Misali, kamar mutane ne da yawa ke cikin daki guda, wanda ya matse su sosai sai aka samu karin daki don rage mutanen. Su wadanda aka rage za su ce maka ba su samu ci gaba ba? A je hankalinka ma, a yanzu ka dubi yadda mutanenmu ke rubuta jarabawar share fagen shiga jami’a (JAMB), mutum nawa ke samu? Cikin ma jami’oin sun yi yawa, da ba a samu yawaitarsu ba, za a sha wahala fiye da yanzu, domin fa muna da yawa a kasar nan. Da a ce Jami’ar Zariya kadai muke da ita, ya za ka kwatanta wahalar shigarta da fadada ta, da kawai mutum zai jira-jira ne ba lokaci don wasu sun mayar da ita tasu. Yanzu haka muna bukatar karin jami’ar kere-kere a nan Sakkwato. Yawaita jami’o’i na kawo bambancin hanyar samun ilmi da tunani da halayya, wadannan ko duk samun ci gaba ne ga rayuwar al’umma. In ka cire rashin tsari mai kyau da kayan aiki, ba wani ci baya cikin yawaitar jami’oi. Idan yara na son yin karatu amma suka kasa samun gurbin karatun, ka san irin halin da za su fada, kan wannan za ka tabbatar an samu ci gaba.”