Ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya?4
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa: Bai dace a kara ba […]
A halin da ake ciki, dalibai sun yi yawa a Najeriya, har ta kai ma a kowace shekara daliban da suka cancanci shiga jami’a ba sa samun gurabe. Shin ko ya dace a kara yawan jami’o’i a Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:
Bai dace a kara ba – Abubakar Isah
Abubakar Isah Sakkwato: “A gaskiya yawan jami’oi a Nijeriya bai samar da komai ba face ci baya. Ka dubi yadda jami’oin da muke da su a kasar nan suke kamar su mutu, amma a hakan dai ake ta tafiya ba yabo ba fallasa, tun ba inganta su ba sai aka rika yi masu kishiyoyi, wanda hakan ta samar da rashin ingantattun malamai a jimi’oin kasar nan. A yanzu kusan dukkan daliban da ke kammala jami’a ba su samu wadataccen karatun da suke iya koyar da dalibi darasi har ya gane shi ma ya iya ilmantar da wani ba. In ka duba yadda tsarin yawaitar jami’oi yake kasar ba wani abu wai shi ci gaba. A kasar nan gaba daya, ni ban san wata jami’a da ke iya daukar nauyin kanta ba, balle har a ce to ita an gama da ita, bari a kirkiro wata ita ma a rene ta har ta kai matsayin ta farko. Don haka yawaita jami’oi yaudarar ilmi da manema ilmi ake yi kawai, hukumomin ilmi sun tabbatar da a halin da ake ciki, yawaita jami’oi ba zai kawo ci gaba ba.”