Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?
Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a […]
Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a Legas da sauransu. A kwanan nan ma, Jihar Legas ta mayar da wasu gajiyayu ’yan kabilar Ibo zuwa jihohinsu na asali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa bai dace ba? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban, kamar haka:
Mayar da su gida rashin adalci ne
– Yusuf Lamsha
Malam Yusuf Lamsha: “A ganina, batun mayar da mabarata ko kuma musakai ya zuwa jahohiinsu na asali da wasu gwamnatocin kasar nan ke yi, hakan ba komai ba ne illa rashin adalci daga shugabannin kasa. Irin wannan dibar karan mahaukaciya da ake yi wa mabarata da musakai, hakan ba komai ba ne illa take musu hakkokinsu ne a matsayinsu na ’yan Adam, wadanda haka Allah (SWT) Ya so ya gansu. Don haka akwai ma bukatar Gwamnatin Tarayya da ’yan majalisun kasa da kungiyoyin kare hakkin ’yan Adam su taka wa wadannan jihohi birki. Akwai bukatar gwamnatoci kuma su samar wa da wadannan musakai abin yi maimakon tozarta su tun da su ma suna da hakki a kan tattalin arzikin kasa, a matsayinsu na ’yan kasa.”