Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?1

Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a […]

Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?1
Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?1

Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a Legas da sauransu. A kwanan nan ma, Jihar Legas ta mayar da wasu gajiyayu ’yan kabilar Ibo zuwa jihohinsu na asali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa bai dace ba? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban, kamar haka:

Mayar da su jihohinsu abune mai kyau – Sa’idu Jibril
Malam Sa’idu Jibril: “Ni ina ganin ba laifi ba ne don wata jiha ta kwashe gajiyayyun da ke jihar ta mayar da su jihohinsu na haihuwa ba, duk kuwa da na san tsarin mulkin kasar nan ya ba wa kowane dan Najeriya damar zama a duk inda yake so a fadin kasar nan. Idan za a ce kowane gajiyayye ko mabaraci ya zauna a jiharsa ta asali, to hakan zai magance irin cinkoson da ake samu nasu a wasu manyan jihohin kamar Legas da Kano. Yanzu ki duba irin yawan da suka yi a nan Kano saboda sun san suna samun sadaka; wannan ba abu ne mai kyau ba. Ina goyon bayan kowa ya tsaya a jiharsa.”

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno