Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?2
Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a […]
Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a Legas da sauransu. A kwanan nan ma, Jihar Legas ta mayar da wasu gajiyayu ’yan kabilar Ibo zuwa jihohinsu na asali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa bai dace ba? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban, kamar haka:
Hakan bai dace da tsarin mulki ba
– Malam Buni Ali
Malam Buni Ali, Shugaban kungiyar Makafin Jihar Yobe: “A ganina, yadda wasu gwamnatocin jahohin kasar nan ke daukar musakai da mabarata ya zuwa jahohinsu na asali, hakan da suke yi tamkar yi wa tsarin mulkin kasar nan ne karan-tsaye ne kuma hakan bai dace ba kwata-kwata. Kowane dan kasa ya san da cewar tsarin mulkin kasar nan ya ba da dama ga dukkan wani dan kasa da ya zauna duk wani bangaren kasar nan da ya ga dama ba tare da tsangwama ba. Don haka, matukar ana son musakai su daina gararamba a titunan jihohin kasar nan, to ya zama wajibi a nema musu abin yi amma in ba hakan gwamnatoci suka yi ba, to babu zabi ga mabaratan illa shiga yin bara, don barar ita ce hanyar da suke bi don samar wa kansu da iyalansu abinci.”