Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?3

Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a […]

Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?3
Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?3

Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a Legas da sauransu. A kwanan nan ma, Jihar Legas ta mayar da wasu gajiyayu ’yan kabilar Ibo zuwa jihohinsu na asali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa bai dace ba? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban, kamar haka:

Bai dace a rika mayar da su gida ba
– Alhaji Umar

Alhaji Umar Abdullahi, Sabo-Ondo, Mai Ba Gwamnan Jihar Ondo Shawara Ta Musamman: “Bai dace a rika tattara mutane ana mayar da su jihohinsu na asali ba, domin su ma ’yan Najeriya ne kamar kowa da suke da damar gudanar da irin rayuwar da suke so. Amma kuma ina ganin wannan zai zama darasi ga gwamnatocinmu na Arewacin kasa da suka yi sake suka bari ana cin mutuncin ’yan uwanmu. Na fadi haka ne domin mafi yawancin gajiyayyu da mabarata har da masu tabin hankali da ake mayar da su jihohinsu na asali sun fito ne daga jihohin Arewa.”

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno