Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?4

Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a […]

Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?4
Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?4

Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a Legas da sauransu. A kwanan nan ma, Jihar Legas ta mayar da wasu gajiyayu ’yan kabilar Ibo zuwa jihohinsu na asali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa bai dace ba? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban, kamar haka:

Idan kowa yana jiharsa zai fi samun kulawa – Muhammad Lawan
Muhammad Lawan: “A ra’ayina, idan kowane gajiyayye yana jiharsa zai fi samun kulawar gwamnatinsa. Kin ga ba ma sai sun shiga yawon bara ba. Idan kuwa aka taru a wata jihar, koda gwamnati na son taimaka wa gajiyayyun da ke jihar saboda yawansu, sai ka ga gwamnatin ta kasa tabuka musu wani abin kirki. A shawarata, kowane gajiyayye ya zauna a jiharsa ko kuma in ce a mayar da shi jiharsa shi ya fi.”

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno