Ko ya dace a rika mayar da gajiyayyu zuwa jihohinsu na asali?5
Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a […]
Ba tun yau ba ne a Najeriya ake nuna wa baki wariya ba, musaman ma dai gajiyayyu da mabarata. Za ka ga an tattara mabarata ko gajiyayyu da suka zauna a wasu biranen kasar nan, an saka su a mota, an mayar da su jihohinsu na asali. An yi haka a Abuja, an yi a Legas da sauransu. A kwanan nan ma, Jihar Legas ta mayar da wasu gajiyayu ’yan kabilar Ibo zuwa jihohinsu na asali. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka, ko kuwa bai dace ba? Wakilanmu sun jiwo ra’ayoyin mutane daban-daban, kamar haka:
Matakin mayar da su gida ya dace
– Yahya Kutunga
Alhaji Yahya Baba Kutunga, Sabo-Ibadan: “Ina matukar maraba da wannan mataki da wasu jihohi suka fara dauka, kuma ya dace kwarai a ci gaba da yin hakan domin zai sa kowace jiha ta san darajar kanta ta fannin yin amfani da arzikinta wajen kyautata kula da raywar jama’arta. Tun farko, kyale irin wadannan mutane suna yawace-yawace a garuruwan kasar nan ba tare da yi musu tanadin rayuwa ba, shi ne ya haifar da karuwar irinsu da suke kwana a kan tituna da wuraren tara shara alhali sun mallaki kyakkyawan matsuguni a kauyuka da garuruwansu.”