Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?

Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka: Rushe gidajen bai […]

Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?
Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?

Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka:

Rushe gidajen bai dace ba – Ustaz Amin
Ustaz Aminu Abubakar: “Gaskiya bai dace a rika rusa gidajen ba saboda ai gidajen a wasu lokuta ba na wadanda ake zargin ba ne. Ita hukuma ai ta san hanyoyin da za ta bi wajen hukunta ko gano masu ainihin wannan gidaje. Domin a mafi akasarin ’yan ta’addar da ake zargi da zama a irin wadannan gidaje da ake kama su a ciki, ai gidan ba nasu ba ne. Mafi yawansu haya suke yi a gidan, ka ga shi mai ainihin gidan kila bai san aiki ko abin da suke yi ba sai idan asiri ya tonu. Saboda haka idan jami’an tsaro suka je kama wadanda ake zargi ko suka yi nasarar kama su, ba zai dace ba idan kuma suka rusa gidan mutane babu gaira babu dalili. Saboda haka akwai bukatar bincike sosai, a maimakon rushe gidajen mutane.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya