Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?1

Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka: A rika bincike […]

Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?1
Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?1

Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka:

A rika bincike kafin a rushe
– Abubakar Muhammad
Abubakar Muhammad: “A ra’ayina, bai dace a rika rushe gidajen da ake zargi na ’yan Boko Haram ba ne, kai koda an tabbatar nasun ne. A maimakon haka, kamata ya yi gwamnati ko jami’an tsaro su zurfafa bincike har a tabbatar da gaskiyar lamari, duk abin da ya kama na hukunci sai a zartar musu da shi. Wasu lokutan ma sai ka ga sai bayan an rushe gidajen sannan daga baya a gano cewa ba gidan aka shiga ba. To ina amfanin irin wannan? Irin wanan aikin da jami’an tsaron ke yi ya sa mutane sun fara shakku cewa shin ma anya akwai gaskiya a cikin batun da ake cewa jami’an tsaro sun sami kayayyakin hada bam a gidajen da ake rushewar? Kamata ya yi hukumar tsaro ta yi kokarin kama su amma ba a rushe gida ba. Idan ma an rushe gidan ba a kama su ba, to ai an kashe maciji ne ba a sare kai ba.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya