Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?2
Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka: Ya saba wa […]
Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka:
Ya saba wa doka – Barista Mohammad
Barista Muhammad Bello Umar: “Rushe gidajen mutane a bisa zargin cewa su ’yan Boko Haram ko kuma maboyar ’yan ta’adda ne ya saba wa dokar kasa, sai dai idan kotu ce ta ba da umarnin yin hakan. Saboda haka ina ganin bai dace ba a ce da zarar an gano wata maboyar ’yan ta’adda, ba tare da an kammala gudanar da cikakken bincike ba, a rusa saboda yin hakan zai sanya a batar da duk wata shaida da za a nema. Wannan ya sa muke ganin bai dace ba a ce da zarar an yi fito-na-fito da jami’an tsaro da ’yan bindiga har suka gudu ko aka kashe su, shi ke nan sai jami’an tsaro su kama rusa gidan ko gidajen da aka yi wannan harbe-harbe; a maimakon su ci gaba da binciken yadda aka yi wadannan ’yan bindiga suka zauna a wannan gida.
“Baya ga haka, Sashe na 44 a Kundin Tsarin Mulkin kasar nan na 1999 ya ba da kariya ga ’yan Najeriya, na kada a matsa masu wajen kwace masu dukiya ko wacce iri ce ba tare da wata alama ko shaida da ke nuna alakar maigidan da aikata wani laifi ba, ballantana har a rusa masa gida. Daga karshe, wannan dabi’a ta jami’an tsaro tana kawo nakasu wajen gudanar da bincike. Don haka bai dace ba.”