Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?4
Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka: A gaskiya bai […]
Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka:
A gaskiya bai dace ba – Hassan Ali
Hassan Ali: “Ina ganin gaskiya bai dace a ce kai tsaye an rushe gidajen nasu ba, koda kuwa an tabbatar cewa su ne a ciki, musamman ma ganin cewa a mafi yawan lokuta gidajen da ake rushewa ma ba mallakar wadanda ake zargi da Boko Haram din ba ne. Yawanci haya suke karba a wurin jama’ar gari kuma shi laifin nan ba a rubuce yake a goshinsu ba ballantana mutum ya hana su hayar gidansa, duk da cewar ana kokarin kiyaye wasu abubuwan amma wani lokacin hakan ba za ta yiwu ba. Ka ga a karshe masu gidan ake janyo wa asara, wadanda kuma wani dalilin talaucewarsa ke nan.”