Ko ya dace a rika rushe gidajen da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki?5
Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka: Ya dace a […]
Hukumomin tsaro a Najeriya sun dauki wata sara, inda suke rushe duk wani gida da ake zargin akwai ’yan Boko Haram a ciki, koda kuwa na haya ne. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika yin haka? Wakilanmu sun tattauna da jama’a daban-daban, ga kuma ra’ayoyinsu kamar haka:
Ya dace a rika rushewa – Alhaji Ado dan’azumi
Alhaji Ado dan’azumi: “A ra’ayina dangane da rushe gidajen wadanda ake zaton ’yan Boko Haram ne da hukuma ke yi da zarar sun samu rahoton hakan, a gaskiya hakan ya dace matuka. Dalili kuwa shi ne, in har muddin ba wannan mataki na rushe gidajen aka dauka ba, to ba fata ba akwai yiwuwar su sake dawowa don gudanar da ayyukansu da ya saba shari’a ciki. “To amma in har aka dauki matakin rushe su, ai ka ga babu batun sake dawowa wannan muhalli nasu.”