Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa?
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. […]
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. Abin tambaya, shin ya dace a soke shi ko kuwa a bar shi ya ci gaba da gudana? Ga abin da al’umma ke cewa:
Ofishin bai da muhimmanci – Nuradeen Maigado
Alhaji Nuradeen Muhammad Inuwa Maigado Takai: “Ofishin Matar Shugaban kasa wata hanya ce da wasu azzalumai suka bullo da ita, domin su samu damar wandaka da dukiyar al’ummar Najeriya. Domin ofishin ba ya cikin tsarin mulkin Najeriya. Idan ka duba, tun daga kan matar Janar Ibrahim Badamasi Babangida har ya zuwa wannan lokacin, babu wata matar Shugaban kasa da matan Najeriya suka amfana da wani abu da ta yi. Ana amfani da wannan ofishi ne kawai ana handame dukiyar al’ummar Najeriya. Don haka a ra’ayina ko waye ya zama Shugaban kasa, ya soke wannan ofishi, don ba shi da wani amfani.”