Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa? 1
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. […]
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. Abin tambaya, shin ya dace a soke shi ko kuwa a bar shi ya ci gaba da gudana? Ga abin da al’umma ke cewa:
Bai kamata a bar ofishin ya ci gaba ba – dahiru Hassan
Malam dahiru Hassan: “Maganar Ofishin Matar Shugaban kasa wani abu ne wanda ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. Dokar kasa ta nuna akwai Ma’aikatar Mata Ta Tarayya da ma’aikatun mata a dukkan jihohin kasar nan. Wadannan ma’aikatu su ne dokar kasa ta amince da su wajen taimakon matan Najeriya. Don haka su ya kamata a bai wa mahimmanci don su taimaki matan Najeriya. Amma maganar ofishin, idan ya zamanto aka ce Shugaban kasa yana da mata hudu, zai kasance ke nan kowace mata za ta sami ofishinta ke nan, a matsayinta na matar Shugaban kasa?
“Wannan wasa da dukiyar al’ummar Najeriya ne ta hanyar da ba ta dace ba. Don haka bai kamata a bar Ofishin Matar Shugaban kasa ya ci gaba da kasancewa ba a Najeriya, musamman ganin ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.”