Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa? 2
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. […]
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. Abin tambaya, shin ya dace a soke shi ko kuwa a bar shi ya ci gaba da gudana? Ga abin da al’umma ke cewa:
Bai kamata a rushe ofishin ba – Hajiya Bilkisu
Hajiya Bilkisu: “Bai kamata a rushe a ofishin ba saboda yana da amfani ga mata. Mafi yawan mata ba za su iya ganin Shugaban kasa ba kai tsaye amma idan suka bi ta ofishin matarsa, kokensu zai kai gare shi ba tare da wata matsala ba. Saboda haka ya kamata a bar ofishin don yana amfanar matan kasar nan. Kuma akwai ayyukan ci gaban mata da yawa da Ofishin Matar Shugaban kasa yake yi a sassa da dama na kasar nan.”