Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa? 3
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. […]
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. Abin tambaya, shin ya dace a soke shi ko kuwa a bar shi ya ci gaba da gudana? Ga abin da al’umma ke cewa:
Bai kamata a rushe shi ba – Jibrin Jibo
Jibrin Jibo: “Ni ina ganin bai kamata a rushe Ofishin Matar Shugaban kasa ba saboda yana taimakawa matuka da gaske. Mata suna bayar da gudunmawar da ta kamata dangane da ci gaban kasa da bunkasar tattalin arzikin kasa kuma idan suna da wani korafi, ta ofishin suke gabatar da shi.