Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa? 4
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. […]
A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. Abin tambaya, shin ya dace a soke shi ko kuwa a bar shi ya ci gaba da gudana? Ga abin da al’umma ke cewa:
Kwaskwarima ya dace a yi wa ofishin – Rabaran dan Amarya
Rabaran Muhammadu dan Amarya: “Maganar Ofishin Matar Shugaban kasa, idan kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da ofishin babu laifi, a yi masa gyaran fuska domin ya tafi daidai da zamani.
“Kamar yadda kowa ya sani ne, muna da kundin tsarin mulki a Najeriya kuma ya yi jawabi game da yadda za a gudanar da harkokin gwamnati. Saboda haka a fahimtata, kada a soke ofishin duk da cewa akwai masu zargin ba a gudanar da abubuwa yadda ya kamata a ofishin. Akwai wadanda suke ganin matar Shugaban kasa tana wuce gona da iri bisa yadda take tafiyar da ofishin tun da ba ita ce aka zaba ba, mijinta ne. Saboda haka abin da zan fada a nan shi ne, a bar ofishin amma ta yi ayyukanta cikin gaskiya da tsoron Allah; wato kwaskwarima ya kamata a yi wa ofishin.”