Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa? 5

A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. […]

Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa? 5
Ko ya dace a soke Ofishin Matar Shugaban kasa? 5

A Najeriya, ana gudanar da Ofishin Matar Shugaban kasa da na Gwamnoni, a wasu jihohin ma har da na matan shugabannin kananan hukumoni. Ana da tabbacin cewa kundin tsarin mulki bai tanadi irin wannan ofishi ba, dalilin da ya sa wasu ke ganin kamar ma bai da amfani, a yayin da wasu ke ganin alfanunsa. Abin tambaya, shin ya dace a soke shi ko kuwa a bar shi ya ci gaba da gudana? Ga abin da al’umma ke cewa:

Bai dace a soke ofishin ba – Munkaila Ajiya
Alhaji Munkaila Ajiyan Burra: “Ra’ayina game da wannan batun shi ne, ni ina da ra’ayin kada a soke Ofishin Matar Shugaban kasa. Sai dai kuma akwai masu ganin ba a gudanar da abubuwa yadda ya kamata a ofishin kuma ya kamata a ce duk wani shugaba akwai mace kusa da shi, domin idan ya yi kuskure ita za ta masa gyara. Matukar akwai mace wacce take da ilimi da hankali da sanin ya kamata, to tabbas za ta ba da shawarwari ma su amfani, wadanda idan aka yi amfani da su ta hanyoyin da suka kamata; to tabbas rayuwar al’umma za ta canza cikin kankanin lokaci.
“Saboda haka wannan ofis na Matar Shugaban kasa, kada a soke shi amma a yi masa kwaskwarima ta yadda zai tafi da zamani.”