Ko ya dace a takaita yawan jam’iyyu zuwa biyu a Najeriya?1
Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, […]
Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kadai ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Na goyi bayan jam’iyyu biyu – Tukur Ibrahim
Tukur Ibrahim Gusau: “Ni a ra’ayina, ya dace ya zama jam’iyyun da za a gudanar a kasar nan su zama guda biyu kawai, domin hakan zai rage rigingimu da yawan tashin hankali kuma zai zama ba a sami rarrabuwar kawunan jama’a da yawa ba. Kuma za a samu rage yawan kudaden da Gwannatin Tarayya take bai wa kowace jam’iyya in dai tana da rajista. Kuma zai rage magudin zabe, kamar kuma yadda zai kawo hadin kai tsakanin jama’ar Kudu da na Arewa a siyasance.”