Ko ya dace a takaita yawan jam’iyyu zuwa biyu a Najeriya?4
Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, […]
Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kadai ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:
Ya dace su dunkule su koma guda biyu
– Malam Musa
Malam Musa Maishinkafa: “Ya dace a dunkule jam’iyyun Najeriya su koma guda biyu, domin ya fi saukin kashe kudi kuma za a fi samun adawa mai inganci; ba kamar jam’iyyu da yawa ba, inda za ka ga wata jam’iyyar ma ba ta da dan takara, wata ma ba ta da ofishi. Mu yin hakan shi zai ba dan takararmu Janar Buhari damar yin shugabancin kasar nan.”