Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya 2 shekara 100 da kafuwa?

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]

Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya 2 shekara 100 da kafuwa?
Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya 2 shekara 100 da kafuwa?

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:

Bikin zancen banza ne – Sulaiman Magaji

Yusuf Sulaiman Magaji: “Duk da cewar dai ba a haife ni ba lokacin da kasar ta hade ta zama Najeriya amma a ’yan
shekaruna da tarihin da na samu, ban ga abin ci gaba a kasar nan da zai sa a yi murna don ta cika shekaru dari ba. Ana murna ne idan an ci gaba amma mu ci gabanmu bai wuce na fama da muke yi da rashin ruwan sha da rashin tsaro da rashin magunguna a asibiti da bala’in rashin aikin yi a tsakanin matasa ba.