Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya 4 shekara 100 da kafuwa?
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:
Ya dace a gudanar da bikin – Sarkin Hausawan Akinyele
Sarkin Hausawan Akinyele, Ibadan, Alhaji Ado Sulaiman: “Ina ganin ya dace kwarai da gaske gwamnati ta gudanar da irin wannan biki na murnar cika shekaru 100 da Najeriya ta yi a matsayin dunkulalliyar kasa. daya daga cikin dalilan da suka sa na goyi bayan yin wannan biki shi ne, tarihi ne mai amfanin gaske ga ’yan baya da za su gano irin gwagwarmayar da shugabanni suka yi a wancan lokaci, kafin kasar ta kai ga dunkulewa. Sai dai, ya kamata a rage yawan kudin da za a kashe wajen gudanar da irin wannan biki.”