Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa?
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:
Bikin bai dace ba – Sulaiman Haruna
Malam Sulaiman Haruna Principal: “Dangane da bikin cikar shekaru 100 da samun kasarmu Najeriya da wai ake so a yi biki a kai, a ganina hakan bata lokaci ne kawai; kasancewar babu wani alfanu da za a iya samu. A halin da ake ciki, kasar nan da al’ummarta ba biki ne a gabansu ba. A’a matsalolin da ke addabarmu ne a gabanmu, musamman kan halin rashin kwanciyar hankali da ake fama da shi da kuma rashin shuganci nagari.