Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 1
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:
Bikin rashin sanin ya kamata ne – Mahmuda Madiri
Malam Mahmuda Madiri: “Ra’ayina dangane da bikin cikar shekaru dari cur da kafuwar kasarmu Najeriya, wanda dole ne a kashe makudan kudi wajen hidimar wannan biki, to a gaskiya in an yi hakan tamkar rashin sanin ya kamata ne kan halin da kasar nan ke ciki; na tabarbarewar tsaro da na tattalin arziki. Kowa ya san da cewar halin da ake ciki kasar nan, ba komai take bukata ba illa kara kaimi kan yadda za a samar da tsaro mai inganci a kowane sashi na kasar; musamman sashinmu na Arewa, inda harkokin tsaro suka gama tabarbarewa.