Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 5

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]

Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 5
Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 5

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:

 

Yana da kyau a yi bikin – Alhaji Audu Bukar

Shugaban Kasuwar Shanu ta Akinyele, Ibadan, Alhaji Audu Bukar Ali: “A ra’ayina, yana da kyau a yi wannan biki na murnar cika shekaru 100 da dunkulewar Najeriya kasa daya tilo. Irin ci gaban da aka samu a cikin shekaru 100 da wucewa, musamman a fannonin ’yancin kai da kirkirar jihohi da kananan hukumomi da samun rundunonin tsaro na kasa da bunkasar harkokin kasuwanci a ciki da wajen kasa da makamatansu, sun isa mu fito mu nuna wa duniya farin cikinmu da wannan matsayi. Rashin shugabanni masu tsoron Allah ne ya sa wasu suke kallon cewa ba a ci gaba a Najeriya ba.”