Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 6

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]

Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 6
Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 6

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:

 

Bikin murnar ya dace – Abdullahi Ubandawaki

Abdullahi Ubandawaki: “Bikin ya dace a gabatar da shi, domin shekaru dari ana zaman kasa daya ba wasa ba ne, duk da wasu matsaloli da ake gani sun taso yanzu na kabilanci ba su isa su kange ganin ci gaban da aka samu tun kafin su taso ba. Shugabanninmu na farko sun yi ta kokarin Najeriya ta dore a matsayin kasa daya mai dukkan ci gaban da ake bukata, to an cika burin daya wanda ya kamata a yi mai biki; don bikin ne zai sa tunanin da wasu ke yi na raba kasar ya ja baya. Kila ma a samu canjin hulda ake da ita a yanzu ta dan Ondo yana kallon dan Katsina a jiharsu kamar ba dan kasa ba, dan Sakkwato na ganin dan Bayelsa a matsayin bako.