Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 7

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]

Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 7
Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa? 7

A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:

Bikin ba ya da amfani – Umar Abdullahi

Umar Abdullahi: “An ce ra’ayi riga, gaskiya ni a ganina wannan bikin ba ya da wani tasiri a wurina, domin matsalolin da ke fuskantar wannan kasar ba wanda aka magance, musamman matsalar tsaro ta addabe mu. Ai da duk kudin da za a kashe wurin bikin kamata ya yi a sanya wa harkar tsaro ko wani abu daban na daya daga cikin matsalolinmu amma ba wai a sanya gaba zuwa kashin kudin da ba wani abu da za a iya nuna wa duniya ba. Najeriya ta cika shekara dari, me take nuna wa duniya na ci gaba balle har ta zo yin biki? To da sake, don wannan bata lokaci ne kawai da yin hasarar dukiyar kasa amma ba wani abin biki balle a zo zuwa aiwatar da shi.