Ko ya dace a yi bikin cikar Najeriya shekara 100 da kafuwa?3
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki […]
A ranar daya ga watannan ne Najeriya a ta cika shekara 100 cif da kafuwa a matsayin dunkulalliyar kasa daya. Bisa ga haka ne Gwamnatin Tarayya ke shirin kashe makudan kudi domin gudanar da kasaitaccen bikin murna a watan gobe. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a gudanar da irin wannan biki a halin da kasar take ciki a yanzu? Wakilanmu sun tattaro ra’ayoyin jama’a kamar haka:
Bikin nan bai dace ba – Ibrahim Sa’idu
Ibrahim Sa’ idu Arab: “Batun gaskiya, bikin murnar cikar Najeriya shekaru dari bai dace a yi ba, domin a shekaru darin nan babu wani kwakkwaran ci gaba da aka samu ta kowace hanya, sannan talakan Najeriya yana mutuwa da yunwa da azabar rashin tsaro, sannan a ce za a yi wani biki. Idan za a yi bikin nan, me za a gaya wa wadanda suka halarci wajen? Ya kara da cewa da a ce kasar ta samu wani ci gaba ne, da za mu yi murna amma kash, maimakon mu yi murna sai dai bakin ciki.”