Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?

A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya […]

Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?
Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?

A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin yin sasanci da shugabannin Boko Haram, ta yadda za a yi musayar fursunoninsu da ’yan matan Chibok din? Wato idan aka saki nasu, su kuma su sallamo matan su dawo gida? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban, kuma ga abin da suke cewa:

Ya kamata a yi musayar
– Malam Abubakar
Malam Abubakar Atiku: “Ina da ra’ayin amincewa da yin wannan musaya, wato, idan ya zama wannan ita ce kadai mafita to, na goyi bayan gwamnati ta sallami ’yan Boko Haram daga wuraren da take tsare da su sannan su kuma su sallamo wadannan ’yan mata da suka sace suka boye a tare da su. Sai dai a yi taka-tsan-tsan wajen aiwatar da wannan yarjejeniya, domin suna iya yaudara bayan mutanensu sun shiga hannunsu su ci gaba da rike ’yan matan. Na amince da yin haka ne domin tausayawa ga wadannan ’yan mata da iyayensu, wato bayan kasancewarsu mata sannan kuma ga su da karancin shekaru.”