Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?1
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya […]
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin yin sasanci da shugabannin Boko Haram, ta yadda za a yi musayar fursunoninsu da ’yan matan Chibok din? Wato idan aka saki nasu, su kuma su sallamo matan su dawo gida? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban, kuma ga abin da suke cewa:
Bai dace a yi musayar ba – Alhaji Yahya
Alhaji Yahya Dauda: “Ni dai a gani na bai dace a yi wannan musayar ba. Idan har Gwamnatin Tarayya ta amince da hakan, sai mu ce ta yi amai ta lashe ke nan, domin tun da ’yan Boko Haram suka sace wadannan ’yan mata gwamnatin take cewa za ta kwato su daga hannun wadannan mutane. Yaya za ta dawo ta ce za ta amince da sallamar ’yan Boko Haram da ake tsare da su a gidajen yari kafin su sako ’yan matan da suka kama? Idan har gwamnati ta amince da yin hakan, ta gaza ke nan. Abin da kawai ya kamata gwamnati ta yi shi ne, ta samo hanyar kwato wadannan ’yan mata daga hannun ’yan Boko Haram.”