Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?2
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya […]
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin yin sasanci da shugabannin Boko Haram, ta yadda za a yi musayar fursunoninsu da ’yan matan Chibok din? Wato idan aka saki nasu, su kuma su sallamo matan su dawo gida? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban, kuma ga abin da suke cewa:
Ya kamata a yi musayar – Alhaji Umaru
Alhaji Umaru: “Gaskiyar magana a nan, ya kamata a yi wannan musayar in za ta kawo zaman lafiya a kasar nan, domin fa ya kamata shugabanninmu su kula da bukatu da muradin al’ummarsu kuma yin shiri ga duk wani abu da zai kawo kwanciyar hankali ga kasa da mutanen kasa. Ya kamata mu sani fa ba mu da wata kasa fiye da wannan in ta zauna lafiya mu ne, don haka ban ga dalilin da zai sa a rika aiwatar da wasu abubuwa na rikita kasa ba. Iyayen wadannan yara da su kansu yaran na bukatar ’yanci kamar kowa, don haka ko ya kamata gwamnati ta yi iya yin ta na ganin ta samar musu da ’yanci.