Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?3
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya […]
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin yin sasanci da shugabannin Boko Haram, ta yadda za a yi musayar fursunoninsu da ’yan matan Chibok din? Wato idan aka saki nasu, su kuma su sallamo matan su dawo gida? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban, kuma ga abin da suke cewa:
Yin musayar ya dace – Nasiru Musa
Nasiru Musa: “A gaskiya a nawa ra’ayi ya dace, domin idan aka dubi halin da daliban da iyayensu suke ciki, don kowa yana da nasa ’yanci dan suma daga cikinsu akwai ’yan Najeriya kuma daga cikinsu akwai wadanda aka tilasta wa shiga cikin wannan kungiyar kamar yadda wani daga cikinsu ya yi magana a wata kafar yada labarai. Uwa uba ma, su kansu sojojin Najeriya kawunansu sun rarraba. Ya dace a yi musayar domin kubutar da rayuwarsu daga hannun ’yan kungiyar. Domin Hausawa na cewa ja da baya ga rago ba tsoro ba ne.