Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?4
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya […]
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin yin sasanci da shugabannin Boko Haram, ta yadda za a yi musayar fursunoninsu da ’yan matan Chibok din? Wato idan aka saki nasu, su kuma su sallamo matan su dawo gida? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban, kuma ga abin da suke cewa:
Ya kamata a yi sasanci da sulhu – Lawan Muhammad
Lawan Muhammad: Wannan batu ne da ya kamata a karbe shi da hannu biyu saboda ina mamaki game da yadda gwamnati ke lakaki kan batun, musamman ganin an fito da hotunan matan nan an nuna an ga zahiri su ne. To a nan ina gani bai kamata a ce an kawo yanzu ba a karbi bukatarsu an yi musayar ba. Saboda hatta Amurka a kwanakin nan mun ga yadda ta yi musayar ’yan Taliban da mutum guda. Tun da dadewa ya kamata a karbi wannan bukata ta ’yan Boko Haram, a ce an yi musayar domin ba wanda ya san inda ’yan matan suke. Su kuma mutanensu da dama na hannu, kuma gwamnati ta sha cewa za ta hau teburin sulhu, ta yi musu yafiya amma har yanzu ana maida lamarin abin wasa.