Ko ya dace a yi musayar fursunonin Boko Haram da ’yan matan Chibok?5
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya […]
A halin da ake ciki a Najeriya, sama da watanni biyu ke nan da ’yan Boko Haram suka kame ’yan matan sakandaren gwamnati da ke Chibok, su kusan 300. Ana ta kai-kawo game da matakin da ya kamata a dauka domin ceto su, amma har yanzu haka ba ta cin ma ruwa ba. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin yin sasanci da shugabannin Boko Haram, ta yadda za a yi musayar fursunoninsu da ’yan matan Chibok din? Wato idan aka saki nasu, su kuma su sallamo matan su dawo gida? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban, kuma ga abin da suke cewa:
Maganar musaya ba ta taso ba – Ahmad Kaigama
Ahmad Kaigama: Abin dubawa shi ne, su ’yan Boko Haram ba wanda zai ce wane ne ko ba wane ne ba a zahiri, don haka ina ganin maganar musaya ma ba ta taso ba. Shi ya sa ni ban goyi baya ba don ba a san da wa za a yi ba. Saboda mutane da yawa aka kama, wadanda ke kungiyar da wadanda ba sa ciki kuma yawanci wasu ba su da hakki ma an kashe su. Amma idan gaskiya ne, Shekau ya fito da mutanensa, gwamnati ta fito da nata a yi magana ta gaskiya, duniya ta gani sai kowa ya gamsu. Saboda wannan na cewa Shekau ya mutu shi kuma yana cewa yana nan da rai bai mutu ba, duk ba mu san me ke faruwa ba; maganganu sun yi yawa. Fatarmu Allah Ya bayyana gaskiya, Ya kawo mana karshen kashe-kashe da ake yi. An jima ana maganar sulhu amma ba wanda zai ce gaskiya ga abin da ake ciki.”